SALLAR QASARU

Sallar qasaru sallace wadda Allah subhanahu watala ya sauqaqawa
matafiyi saboda wahalar datakecikin tafiya, Allah yabada damar gajarta
sallah mai raka'a hudu izuwa biyu.
Kamar yadda yake fada acikin alqurani mai girma cikin suratul nisa'i ayata
101
"Kum aidan kunyi tafiya acikin ƙasa to, bãbu laifi akanku kurage daga
salla idan kunji tsõron waɗanda suka kãfirta sufitineku..."
Anruwaito hadisai dadamagameda adadin kwanakin daya kamata ayi
ana sallar qasaru wasu daga cikin magabata sunce kwana 3, wasu kuma
kwana 4, wasu sunce kwana10, wasu sunce 15, wasu sunce kwana19,
 wasu sunce kwana20, wasuma sunce wata shida, wasu kuma sunce
matuqar kana daniyyar dawowa garinku baka qaura gaba dayaba kanada
niyyar komawa gida to zakayi qasaru. Kowane malami yanada
qwaqqwarar hujja daga hadisan Manson Allah akan maganarsa.
Anyiwa Dr. sani Rijiyar Lemo tambaya akan adadin kwanakin qasaru yace
shi dai aduk karatunshi baiga inda akace ga adadin kwanakin ba shiyasa ma tunda yaje
madina karatu har yadawo duk shekarun da yayi qasaru yake.
Allah ne masani

Comments

Popular Posts