IDAN HAR LALURA TA HANAKU AZUMTAR RANAR ARAFA TO KAR KU DAMU
IDAN HAR LALURA TA HANAKU AZUMTAR RANAR ARAFA TO KAR KU DAMU.
Lallai kam Annabi (s.a.w) yace :
"Azumin Ranar Arafa yana sanya Allah ya share laifukan shekaru 2, (shekara wacce ta wuce da wacce zata zo) . "
Lallaikam, Dole ne kowa yaso a yafe masa zunubban shekaru 2.
Amma wasu ba zasu sami damar yin Azumin ba saboda wasu dalilai na lalurori.
Da ace Babu dalilin, lallai kam ina kyautata musu zaton INSHA ALLAHU zasu iyayin Azumin .
»» Wasu Ba su da lafiya
»» Wasu kuma sunayin Al'ada.
»» Da makamantan haka.....
KARKU DAMU KUMA KARKU FITAR DA RAN SAMUN LADAN AZUMI DUK DA CEWAR KU BAKUYI AZUMIN BA.
Na san wasu zasu yi ta bakin cikin RASHIN azumtar Wannan rana mai tarin Albarka da Falala ta ARAFA, suna ganin ai kamar duk tarin falala da Lãdaddakin da ake samu a cikin wannan Rana ga duk wanda ya Azumceta, to ya wuce su kenan,,,,!
Sai nace muku A'AH tukuna dai .....
Nasan zaku iya cewa ina Dalili?
Ni kuma sai nace :
Annabi (s.a.w) yace :
"Duk wanda yaciyar da mai Azumi to shima yanada kwatankwacin Ladan mai Azumin ba tare da an rage wa mai Azumin komai daga cikin Ladansa ba. "
Sahih At-Tirmidhy.
Na SAN WANI ZAI CE :AI NI BA NI DA DAMAR CIYARWA
Ai Babu damuwa saboda Ba sharadi bane sai ka ciyar da abinci da mutum zai koshi shine ka ciyar da mai Azumi ba.....
Kar kamanta ka fahimta cewar Ko Dabino ne ko Ruwa da makamantan su kaba wa mutumin da yayi Azumi to tamkar ka ciyar da shi ne.
Allahu A'alam
Kamar yadda Al-Allãmah Sheikh Muhammad bin sãleh Al-uthymeen yafada a cikin Fatawowinsa.
YA DAN UWA DA YAR'UWA MASU ALBARKA
Kar kubari wannan rana ta zo ta wuce haka kawai.... To ka zamo cikin masu yin Azumi ko masu Ciyar da masu yin Azumi, domin dacewa da ladan.
YA ALLAH KA AMSA IBADUN MU, KUMA KA YAFE MANA ZUNUBBANMU BÂKI DAYA, SANNAN KUMA KASANYA MU CIKIN WADANDA KAKE 'YANTAWA A WANNAN RANA.
Ameen
Comments
Post a Comment