KARATUN YANKA DABBAR LAYYA

ME AKE FADA YAYIN YANKA DABBA?

Manzon Allah(s) cewa yayi:

باسم الله اللهم تقبل من محمد وآل محمد.
"bismillahi Allahumma taqabbal min Muhammadin wa ali Muhammadin"
(Muslim).

A cikin (Musnad da Sunan na Abu Dauda) kuma cewa yayi:

باسم الله والله أكبر.
"bismillahi wallahu akbar"

Don hakane sai Mallam Nawawi a cikin Sharhin Hadisin Muslim yace:

"فيه دليل لاستحباب قول المضحي حال الذبح مع التسمية والتكبير اللهم تقبل مني"
"a cikin sa akwai dalilin mustahabbanci fadar mai yanka dabbarsa ta layya yayin da ya ambaci Allah, kuma yayi kabbara sai yace: Allahumma Taqabbal Minni".

Lafazin zai kasance kamar haka:
BISMILLAHI WALLAHU AKBAR, ALLAHUMMA TAQABBAL MINNI ko kuma (MINNA).

Kamar yadda yazo a cikin RISALAH ta Mallam Abu Zaidi Al-qairawani.
Ko kuma:

للهم هذا عني وعن أهل بيتي
Allahumma haza Anni wa an ahli baiti.

Ko kuma:

اللهم تقبل مني ومن أهلي
Allahumma taqabbal minni wa min Ahlii.
Ko kuma ka ambaci sunanka misali kace:

للهم تقبل من فلان وآل فلان.
Allahumma taqabbal min..... wa Ali.....

Wallahu a'alam.

Comments

Post a Comment

Popular Posts