LAYYA
Daga: Dr. Jabir Sani Maihula Hafizahullah
1) Layya wajibi ce gurin wasu Malamai, wasu kuma na ganin ta Sunnah mai karfi.
2) Layya ibadah ce mai karfi mai zaman kanta, bata da alaka da sai mai aure ko sai mai kudi. Duk wanda yake da abin yankawa ya wajaba /kamata ya yi. Akwai dalilai da ke nuna Sahabban Manzon Allah S. A. W. sukan yi Layya basu da abincin Sallah.
3) Mutum bakwai suna iya hada kudi su sayi saniya daya su yanka. Idan kowa zai bada 20K ko abinda bai kai hakan ba, zasu iya Layya kowa ya samu lada.
4) Layyah tafi karfi kuma tafi lada akan dinka tufafin sallah. Da ka dinka tufafin Sallah na N50K gara kayi Layya da kudin.
5) Idan kana iya sayen wayar hannu ko Dunkin tufafi na N50K amma ba zaka iya hada N20K da abokanin ka ku sayi abin Layya ba, ka binciki (priority) abinda kake fifitawa tsakanin duniyar ka da lahirar ka.
Allah Ya sa mu dace, Ya kar ba mana.
Comments
Post a Comment